Yadda ake rubuta wasikar soyayya


Yadda ake rubuta wasikar soyayya
Rate this post

Yadda ake rubuta wasikar soyayya, How to write the letter of love. Wasikar soyayya wata hanya ce ta aika sako zuwa ga wanda ka ke so domin isar masa da abinda ke cikin zuciyarka a rubuce.

 

Letter of love is a method of sending a message to your love one in a written form to deliver the secret of your heart.

 

Akwai hanyoyi da dama da ake bi domin rubuta wasikar soyayya, daga ciki akwai rubuta wasikar soyayya a takarda, rubuta wasikar soyayya a waya da sauransu.

Yadda ake rubuta wasikar soyayya

A duk lokacin da za ka rubuta wasikar soyayya kana bukatar ka san ai nahin abinda ka ke son fada, ma’ana sakon da ka ke so ka isar kai tsaye.

Daga nan kuma sai ka san salon da za ka yi amfani da shi wajen rubuta wasikar soyayya din.

Da zarar ka fahimci wadannan abubuwa to sai kuma ka fara rubuta wasikar soyayyarka cikin kwanciyar hankali.

Kaidojin da aka bi wajen rubuta wasikar soyayya

Kamar kowace wasika, ita ma rubuta wasikar soyayya na da wasu kaidojin da ya kamata a bi domin rubuta ta, kamar yadda za mu gani a kasa:

  • Gabatarwa:

Abu ne mai muhimmanci ka gabatar da kanka kafin ka fara zayyano sakonnin da ka ke so ka isar da su a cikin wasikar soyayyarka.

Idan a waya ne za ka rubuta wasikar soyayya to baka bukatar Adireshi da kwanan wata a farko domin hakan bai zama tilas ba.

Kawai ka fara da sallama da kuma sakon gaisuwa mai jan hankali, wannan ma ya wadatar.

Misali: Salam, bayan gaisuwa mai dauke da tarin alheri ina fatan kina cikin koshin lafiya.

  • Gundarin sako

Bayan sallama da kuma gabatar sai kuma ka takaita domin kar ka isheta da surutai tun kafin ta ji abinda wasikar ta kunsa har ta ji komai ya fara isarta.

A nan akwai bukatar ka yi amfani da salo mai kyau domin hakan ne zai baka damar yin nasara a abinda ka ke nema a wurinta.

Misali: Na rubuto wannan wasikar ne domin ita ce hanya mafi sauki a gare domin isar da sakon da a cikin zuciyita a gareki.

Hakika tun lokacin da na fara tozali da ke na fahimci kyawawan dabi’u da kuma halayenki.

Bugu da kari a yayin da na yi duba izuwa ga yadda ki ke tafiyar da rayuwar ki sai na gano hakika ki na da karamci, da mutunci, da kirki, da halacci a cikin halayenki.

Wannan ne ya tabbatar min da cewa dukkan wanda ya sameki to ya gama samun babban rabo, sai dai kawai ya jira lahirarsa ta yi kyau.

A saboda haka na miko miki linzamin zuciyata domin ki ja ni izuwa ga kyakkyawar rayuwa a cikin wannan kyawawan dabi’un naki.

Da fatan dai zan kasance mutum na farko da zai amfana da karamcinki ta wannan fanni.

 Karanta: Soyayya text message

To a nan ka gama rubuta wasikar soyayya a cikin salo mai kyau kuma mai jan hankali.

Abu na gaba shi ne kammalwa ko kuma katsewa.

  • Kammalawa a yadda ake rubuta wasikar soyayya

Bayan ka  kammala rubuta wasikar soyayya sai kuma ka dauki mataki na karshe a wasikar wanda shi ne rufewa.

A wannan bangaren kuwa bayan ka gama isar da sakon soyayyarka, sai kuma ka rufe wasikar ka da bayyana waye kai domin wadda ka rubuta wasikar a gareta ta san wa ye ya rubuto mata wasikar.

Misali: Ni ne mai sonki har a cikin zuciya Ahmad Bugaje.

To kaga kenan a nan ne ka fayyace mata kanka duk a cikin wasikar taka.

Idan a takarda ne to za ka iya rubuta lambar wayar ka domin ta kiraka ko wani abu makamancin haka.

Join our WhatsApp channel: Kundin masoya

One comment on “Yadda ake rubuta wasikar soyayya

[…] Karanta: Yadda ake rubuta wasikar soyayya […]

Leave a Reply