Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace


Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace
Rate this post

Yadda ake rubuta wasikar soyayya domin sace zuciyar mace, wasikar soyayya ba sabon abu ba ne a duniyar masoya.

Tun zamani mai nisa da ya shide masoya ke amfani da fata, da ganye, har zuwa zamanin takarda domin domin isar da sakonnin soyayya zuwa ga wadanda su ke so.

Ita wasikar soyayya takan taimaka ne wajen isar da sakon da ke da matukar nauyin isarwa a wasu lokutan.

Sau da dama wasu na amfani da wasikar soyayya ne domin neman soyayya da kuma bunkasa ta.

Salon rubuta Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace

Masoyi na iya fuskantar wadda ya ke so kai tsaye domin isar da sakon soyayyarsa ba tare da bin wata doguwar hanya ba, amma kuma a wasu lokutan hakan na iya kasancewa abu mawuyaci.

Karanta: Yadda ake rubuta wasikar soyayya

Idan har wadda za ka isar da sakon so a gareta ya kasance tana da matukar kwarjinin da har ya sanya maka shakkar tinkararta kai tsaye to wasikar soyayya domin sace zuciyar mace ya kamata ka rubuta mata.

Ga kuma salon da ya kamata ka yi amfani da shi kamar haka

  • Ka yi amfani da kalmomin yabo a gareta da gidansu da danginta.
  • Ka yi amfani da kalaman yabon halitta domin ka yaba irin kyawunta ko da bata da shi.
  • Ka yi amfani da kalaman kambamawa domin ka kambamata ta yadda za ka sanya ta a tarko domin kar ta tsallake tayinka tare da toshe mata baki daga watsa maka kasa a ido a kan bukatunka.

Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace a rubuce

Kamar yadda mu ka zayyano a matakan mu na sama, yanzu za mu yi kokarin sanya komai a rubuce kamar yadda za mu gani a kasa:

Assalam,

Bayan sallama irin ta addinin Musulunci tare da fatan alkhairi a gareki.

Ga dukkan wanda yake son samun mace ta gari muddin ya yi tozali da ke tabbas ba zai iya tsallake ki ba.

Dalilin fadar hakan kuwa shi ne irin yadda naganki da kyautatawa, da tausayi, da girmamawa, da kuma kirki.

Abunda ya fi jan hankalina zuwa gareki shi ne yadda naga mutunci a dabiarki, naga karamci a halayyarki, naga kyautayi a muamalarki, sannan kuma na ga alkunya a muamalarki.

Wannan ba wani abun mamaki ba ne musamman ma ga wanda ya san gidan da ki ka fito.

Na tabbata duk macen da ta fito daga babban gida irin na ku ba wani bukatar a yi bincike a kansa kafin a tabbatar shi mutumin kirki ne, domin gidanku babban gida ne.

A saboda haka ina fatan zan ci albarkacin kyawawan halayenki da kuma mutunci da karamci irin na family dinku domin samun amsuwa a gareki.

Daga mai kaunarki, Jalaluddeen Jarumi.

Join our WhatsApp channel: Kundin masoya 

One comment on “Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace

[…] Karanta: Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace […]

Leave a Reply