Quotes of love: Kalaman sace zuciyar masoyi


Kalaman sace zuciyar masoyi
Rate this post

Kalaman sace zuciyar masoyi sace zuciyar masoyi means love quotes for snatching one you love.

Being it so difficult to attract someone to fall in love with you doesn’t mean that you will never earn their affection.

Kalaman sace zuciyar masoyi na nufin kalaman sace zuciyar wanda ka ke so.

Duk da yana da matukar wahala ka ja hankalin wani ya fada soyayya da kai amma hakan ba yana nufin cewa ba za ka samu soyayyarsa ba.

yin amfani da kalaman sace zuciyar masoyi abu ne da zai baka damar yin nasarar samun zuciyar wanda ka ke kauna.

Kalaman sace zuciyar masoyi cikin sauki

A duk lokacin da ka afka soyayyar wani ko wata to fa mawuyaci ne ka kasa yin yunkurin samun tasa/tata soyayya

A wannan yanayin kana bukatar yin amfani da kalaman da ka san za su ja hankalin wanda ka ke so shima ko ita ma ta kware maka. Ga kalaman sace zuciyar masoyi kamar haka:

Kalaman sace zuciyar masoyiya

Assalam ranki ya dade, da farko dai zan a ce na burge ki kamar yadda ke ma ki ka burge ni tun kallon farko da na miki.

Duk da na san hakan mawuyacin abu ne, amma nasan mace mai annuri a fuskar ta dole ta kasance da karamci, da mutunci, da kirki kamar dai yadda ki ke.

A saboda haka ina neman ki bani dama in gabar da kaina tare da zayyano miki muhimman dalilan zuwa na wurin ki .

Ki sani cewa annurin da na gani a fuskar ki sun gama bani labarin ke irin matannan ne da aka bada labarin su a cikin Qurani cewa su na kama da matan aljanna.

Kin ga kuwa tunda haka ne duk wanda ya sameki ya gama samun babban rabo sai dai kawai ya jira lahirarsa ta yi kyau.

Nasan kyawawan mata irin ku dole ne a sameku da tarin masoya na kirki da kuma wanda wasa ya kawo su ko dan a ce su na tarayya da kyakkyawa.

Saboda haka zan zo ki bani dama domin ni ma na shiga cikin jerin na kirkin tare da baki yakinin a sannu za ki aminta da ni ko dan kasancewata masoyi na gaskiya.

 

Kalaman sace zuciyar masoyi

Kasancewar an san matan malam bahaushe da alkunya, ba lallai ne idan kin ga saurayi dan gaye sai ki ka ji kin kware masa to fa ba shiru za ki yi ba har ya subuce miki.

Akwai abubuwa da dama da za ki yi domin yi masa signal na cewa kin kyasa kuma kina ciki ba tare da kin zubar da ajinki na ya mace ba.

Shi namiji yakan gane mace tana sonsa ne idan tana yi masa wasu alamu misali kamar yi masa magana duk inda su ka hadu.

Yawan yi masa murmushi idan sun hada ido daga nesa ko a kusa da juna.

da dai bashi duk wata dama da ta dace domin ya fahimta ana sonsa din.

A saboda haka yanzu duk mun ga wasu hanyoyi da za mu yi amfani da kalaman sace zuciyar masoyi.

Saboda haka mu na fatan wannan zai taimaka wa masu son son kulla alakar soyayya wajen yin nasara a yakin so.

Please feel free to Contact Us       

If you have any questions.

One comment on “Quotes of love: Kalaman sace zuciyar masoyi

[…] Karanta: Quotes of love: Kalaman sace zuciyar masoyi […]

Leave a Reply