Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya


kalaman soyayya masu ratsa zuciya
Rate this post

Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya su ne wasu nau’in kalamai da masoya ke furtawa junansu a yayin da su ke hira domin farantawa tare da burge juna.

Ita soyayya tana ginuwa ne ta hanyar amfani da salo daban daban kama daga salon cin gayu, da hidimtawa juna, da kuma amfani da Kalaman soyayya masu ratsa zuciya.

A nan kafin mu kawo wadannan kalamai ga wasu abubuwan lura kamar haka:

  • Kar ka yi amfani da kalamai masu karin gishiri domin burge wanda ka ke so.
  • Ka guji yin amfani da tsaffin kalaman soyayya irin su ya ke bututun mazurarin zunzurutun zinaren zuciyata, domin su kan sa mace ta kalli kalamanka tamkar tatsuniya.
  • Ka Guji amfani da alkawura a cikin kalamanka, domin hakan na iya sanya ka yin karyar da za ta zama matsa a soyayyar ka.
  • Kar ka yawanta zuga masoyiyar ka har ta kai ga ta fara jin ta fi kowa domin hakan na sa mace ta fara jin ta wuce ajinka.
  • Kar ka nuna mata soyayya a fili har ta fara jin ko ta maka wani laifi soyayya ba za ta bari ka hukunta ta ta ba, yin hakan na jawo ta rena ka ta rika ja maka aji.

Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya

Wadannan kalamai ne na soyayya masu ratsa zuciyar masoya kamar haka:

Sweet heart ki sani cewa a duk lokacin da na ke a tare da ke wani yanayi mafi dadi na ke ji, wannan shi ne dalilin da ya sa na gamsu cewa kina iya kokarinki wajen faranta mini, in fatan za ki kara kaimi a kan hakan.

Hakika ina matukar alfahari da samun ki a matsayin abokiyar rayuwa, domin kyawawan halaye su ne abin da ke kara bani nishadi a tare da ke.

Honey, kina da kyawawan halaye da su ka hada da hakuri, da kyautatawa, da kulawa, da kuma jan hankali, hakika nasan na yi dace da abar kauna.

Haka dai za ka ci gaba da yabon ta domin wannan su ne nau’in kalamai da ke ratsa zuciya sosai.

Karanta: Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya

One comment on “Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya

[…] Karanta: Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya […]

Leave a Reply