kundin masoya part 1 complete


Kundin masoya part one complete
Rate this post

kundin masoya wani kundi ne da ke dauke da dukkan ababen da masoya ke buƙata domin yiwa soyayya banruwa.

a yayain da masoya su ka yi ninkaya a duniyar soyayya abu mafi girma a rayuwarsu shi ne baiwa juna kulawa ta fuskoki daban daban.

A nan za mu yi bayani ne kan wasu sirruka da ya kamata masoya su ke yin la’akari da su domin bunƙasa rayuwar soyayyar su.

  • da farko dai dukkan masoyi na gaskiya ba zai so a ce ya zama silar bacin rai da damuwa ga abokin soyayyar sa ba.
  • Sannan kuma duk inda masoyi na gaskiya ya ke za ka sameshi da kokari wajen faranta ran wanda ke sonsa.
  • Sauda dama a soyayya akan samu banbancin ra’ayi da na fahimta, amma kawar da wannan banbanci shi ne abu mafi alkhairi ga masoyan da su ke son soyayya mai dorewa.
  • Yarda da juna shi ne ginshikin zaman lafiya mai dorewa a soyayya, idan har wani bangare bai yarda da wani ba ko kuma yana zargin wani to nan ma an hau hanyar rusa kauna.
  • Dole ne masoya su yarda da junansu radi bisa dari tare da yiwa juna kyakkyawar fahimta, akasin haka na iya jawo rugujewa kauna.

kundin masoya kalaman soyayya

Soyayya tamkar wani ginshiki ne ko mataka zuwa ga auratayya da kuma samar da iyali.

A duk lokacin da soyayya ta shiga tsakanin saurayi da budurwa, to abinda a ke sa rai daga karshe shi ne aure da hayayyafa domin samar da cikakken iyali.

A saboda haka abu ne mai matukar muhimmanci a duk lokacin da masoya ke kokarin gina rayuwar su a ke so su gina ta bisa tubalin gaskiya da gaskiya da kuma amana da yardar juna.

Karanta: Love: Kalaman soyayya masu ratsa zuciya

Idan har aka samu matsala akan hakan to fa ku sani ko an yi auren rayuwar da za ta biyo baya ba lallai ne ta kasance abar burgewa ba.

Join our WhatsApp channel: Kundin masoya

One comment on “kundin masoya part 1 complete

[…] Karanta: kundin masoya part 1 complete […]

Leave a Reply