Kalaman soyayya na kwanciya bacci


Kalaman soyayya na kwanciya bacci
Rate this post

Kalaman soyayya na kwanciya bacci domin sanyaya ran masoya tare da karawa juna kaimi a duniyar soyayya.

Rayuwar soyayya ta kasance rayuwa mafi dadi a tsakanin maza da mata, a duk lokacin da na miji da mace su ka kulla wata alaka ta soyayya, burin su shi ne farantawa juna.

Haka kuma akwai kalaman na kwanciya bacci wanda masoya kan yi amfani da su wajen fatawa junansu a waya ko ta text.

A nan kuma za mu yi kokarin kawo muku wasu sabbin tsararrun kalaman soyayya na kwanciya bacci domin farantawa juna.

Kalaman soyayya na kwanciya bacci

A yayin da mutum ya kwanta yana jiran zuwan bacci, a wannan ne wani dan takin lokaci da zai zurfafa cikin tunani.

Saboda haka idan ka turawa masoyinka sakon soyayya a irin wannan lokacin zai bashi reaction mai faranta rai sosai.

Bugu da kari a ayayin da da kalaman soyayyar ka su ka zama abu na karshe ga aboki ko abokiyar soyayyarka kafin bacci, hakan zai sa ya ko ta tashi da kai a cikin ranta.

Ga wasu kalaman soyayya na kwanciya bacci kamar haka:

Ya ke habibiya ta, ki sani cewa dare Allah ya yi muna shi ne domin mu huta.

A irin wannan lokacin a kowace rana nakan natsu domin kallon kyakkyawar surarki a cikin raina, ba zan gushe a cikin wannan yanayi ba har sai na yi bacci cikin shaukin so.

Ki sani cewa ke ce mai debe min kewa a cikin bacci ta yadda ko a mafarki nakan ganmu ni da ke a cikin duniyar masoya mai dauke da furanni launi daban-daban.

Sannan kuma ga wasu tsuntsaye na rera wani sauti mai daɗin gaske, nakan ganmu muna shakar kamshin furanni cikin shauki irin na so da kauna.

Karanta: Wasikar soyayya domin sace zuciyar mace

Hakika sweet heart kasantuwar mu a tare a karkashin inuwar soyayyar ba karamin farin ciki zai haifarwa rayuwar mu ba.

Ina fatan za ki yi bacci da ni a cikin zuciyarki kamar yadda ni ma na ke yi, fatan alkhairi a gareki honey sai da safe.

Join our WhatsApp channel: Kundin masoya

0 comments on “Kalaman soyayya na kwanciya bacci

Leave a Reply