Kalaman so da kauna masu ratsa zuciya


Kalaman so da kauna masu ratsa zuciya
Rate this post

Kalaman so da kauna masu ratsa zuciya: wannan wasu nau’in kalamai ne da masoya ke amfani da su domin daskarar da son da a ke musu a cikin zuciyar mai son su.

Kalaman soyayya gajeru na da matuƙar tasiri a zuciyar mace, sannan kuma a zuciyar namiji kalaman soyayya masu zafi sun fi masa tasiri

Wani lokacin ma murmushi da sassanyar murya su kan kalaman soyayya ratsa zuciyar namiji.

Kalaman so da kauna masu ratsa zuciya

Idan har kana son mace sannan kuma kana da burin faranta mata rai, dole ka ke furta mata kalaman so da kauna masu ratsa zuciya.

Matsalar da ake samu ita ce, wasu na cika gishiri a yayin furta irin wadannan kalamai na so da kauna.

Abu ne mai matukar muhimmanci ka san yadda za ka furtawa budurwarka kalaman soyayya .

Ga yadda zaka furta kalaman so da kauna masu ratsa zuciya ba tare da ka wuce gona da iri ba.

Ya ke annurin zuciyaya, hakika yadda ki ke girmamani na bani karfin gwiwar autenki, domin nasan ke kadai ce wadda za ta kula da ni tamkar uwa da jaririnta.

Samun mace mai kishin masoyinta ba karamar Sa’a ba ce domin yakan na nuni da cewa za ta rike maka amanar ka.

Karanta ta: Quotes of love: Kalaman sace zuciyar masoyi

Gashi kuma ni na yi nasarar samun mai kishi na saboda haka ne duk lokacin da na kalleki sai wani sanyi ya kwaranyo a cikin zuciyata.

Da kalamai irin wannan za ka ci riba biyu, da farko dai ka yi amfani da wani salo da zai sa ta yi kishinka, ta kuma rike maka amana.

Sannan kuma ka yi amfani da salon da zai sa ta ke girmamaka, wanda hakan zai sa a samu respect da zai hana afkuwar raini a tsakaninsu.

Haka kuma kalaman naka za su bata nisha di sosai domin za ta ji kana zuga ta kana fasa mata kai wanda su kuwa mata su na son su ji ana zuga su ana yabonsu.

Join our WhatsApp channel: Kundin masoya

0 comments on “Kalaman so da kauna masu ratsa zuciya

Leave a Reply