Just for love: Zafafan kalaman soyayya


Just for love Zafafan kalaman soyayya
Rate this post

Zafafan kalaman soyayya are some words pronounce by someone who is in love. This words that are pronounced are just for love.

Zafafan kalaman soyayya su ne kalaman da mai so ke furtawa ga wanda ya ke so ba dan komai ba sai dan faranta masa rai tare da burgewa.

Zafafan kalaman soyayya na sabbin masoya

Sau da yawa zamantakewar masoya kan banbanta daidai da yanayin yadda su ka saba da juna.

Wannan banbancin na bukatar a yi la’akari da shi wajen furta Zafafan kalaman soyayya.

Dalili kuwa shi ne, masoyan da su ka da de su na son junansu ba daidai su ke da wadanda su sabbi ne a tarayyar so da kauna ba.

Ga wasu Zafafan kalaman soyayya na sabbin masoya kamar haka:

Zafafan kalaman soyayya domin yabon masoyiya

A duk lokacin da na tuna da ke a duk inda na ke, nakan ji wani farin ciki na musamman matas misaltuwa a zuciyata.

Wannan ne dalilin da ya sa na ke yawan tunawa da ke a ko da yaushe.

To a nan saboda soyayyar ku sabuwa ce akwai bukatar ka yi amfani da kalamai na yabo domin ka kara kama zuciyarta kamar haka:

Hakika kyawun da Allah ya miki ba irin na sauran kyawawan mata ba ne, domin ni ke ce kadai na ke iya gani da kyau fiye da dukkan sauran mata.

A duk lokacin da ki ka yi murmushi fararen hakoranki na kara fito da irin kyawun da Allah ya miki ta yadda ko makiya in sun gani sai sun ji su na so ki kara irin sa.

Karanta: Quotes of love: Kalaman sace zuciyar masoyi

Haka dai za ka ci gaba da amfani da kamanninta kana yabonta amma kar ka yawanta.

Daga lokacin da ka fuskanci akwai murmushi da nishadi a fuskar masoyiyar taka sai kuma ka yi kokarin canza salo dan kar ka yi wani cushe da zai kwafsa maka .

da fatan wannan salon zai gamsar da sabbin masoya wajen tsara ababen kaunar su har ya kaisu ga nasara a soyayyar su .

 

0 comments on “Just for love: Zafafan kalaman soyayya

Leave a Reply